JAGORA NA, NA ADDINI SHEIKH MUHAMMAD NUR DASS (H).
باسمه تعالى
√ Daga cikin kokarin wakilin Sayyed Ali Khamnei (DZ) janibin shari'a wato Samahatu Sheikh Nur Dass (H) a Nigeria akwai:
~ Assasa Mu'assasar RASULUL A'AZAM FOUNDATION (RAAF) Mu'assasa ce ta Shi'a Zallah tare da yima wannan Mu'assasar rijista a hukuman ce.
~ Rasulul A'azam Foundation (RAAF) Mu'assasa ce dake bude makarantun Hauzozin ilimi da markazozi dan yada addinin musulunci cikin shi'anci tsantsa.
~ Tana da Makarantun Hauzozi a jihohi daban daban a fadin Nigeria kuma duka makarantu ne masu rijista.
~ Tana da kebantaccen sashe na abinda ya shafi kira da tabligh, wannan sashe ya tara muballigai dayawa a karkashin shi, duka dan Isar da sakon Ahlul-bayt (AS) a fadin Nigeria, Shugaban wannan sashe shine Hujjatul Islam wal muslimin Shekh Bashir lawal kano, wanda ake masa laqabi da Sautush~shi'a.
~ Haka nan wannan shugaba kuma wakilin Sayyed Ali Khamnei (DZ) ya assasa babban Hauza a cikin birnin kano, sunan wannan Makaranta HAUZATU BAQIRUL ULUM wanda shi ke jagorantar wannan makaranta, an samu daga 'Dalibai wadanda suka sha karatu suka fita suma Suna taimakawa a 'bangaren tabligh.
√ Daga cikin kokarin da yayi a bangaren siyasa da janibin jama'a kuma:
1. Yada abinda ya shafi wayewa tsakanin jama'a da abinda ya shafi siyasa, yayi haka ne wajen farkar da 'yan shi'ar kasar wajen shiga cikin al'amuran daya shafi qasa kuma ayi dasu sbd suma 'yan kasa ne.
2. Wayar da kan 'yan shi'a akan abinda ya shafi mahimmancin siyasa, yin zabe da fitowa a zabe su kamar sauran 'yan qasa da sauran Kungiyoyi.
3. Kokarin shi na hadin kai tsakanin Qungiyoyin Musulunci da 'yan shi'a suma a junan su, ya taka rawar gani a wannan janibi.
4. Gusar da mummunan ganin da hukuma take yiwa 'yan Qungiyar daga 'yan tawaye kuma masu taka doka, zuwa 'yan kasa na gari masu kishin kasar su.
::: Akwai kuma kokarin shi na tarwatsa shirin wahabiyawa da suke na kokarin 'bata sunan shi'anci a cikin kasa, tare da sauran daukan mataki da suka dace ta 'bangaren hukuma.
::: kuma Alhmdlh ya samu nasara sosai a wannan yunquri nashi.
5. Karantar da aqidar shi'anci yadda yake asali a musulunci tatacce tsaftatacce daga ruwayoyin da wahabiyawa suke kawowa na qarya, tare da nisantar dashi daga kaucewa tsari.
6. Wannan Mu'assasa ta RASULUL A'AZAM FOUNDATION (RAAF) ta gina Masallacin Shi'a na Juma'a wanda shine farkon masallacin Shi'a a kaf Nigeria, sannan an Gina shi bisa tsari da Neman izinin hukuma, wanda aka Gina shi a Dawanau dawakin tofa dake kano Nigeria.
~ Masallaci ne babba wanda a gefen shi an Gina ajujuwa dan karantarwa da babban dakin taro wato (Hall) da bandakai domin ciyar da shi'anci gaba.
~ Akan gabatar da salloli biyar na yau da kullum a cikin shi, da sauran ibadoji da tarurrukan addini.
7. Tura adadi mai yawa na 'Dalibai makarantun Hauza domin ci gaba da karatun su na addini da samun ilimi mai zurfi.
~ Ya taimaka wajen qarfafawa matasa da taimaka musu domin ci gaba da Karatun jami'a, kuma Alhmdlh dayawa sun amfana da wannan abin alkairin haka har yanxu wasu Suna amfana.
~ Yana Daga cikin abun da yayi: kiran shi da yayita yi tsakanin hukumar Nigeria da Harkar Musulunci a Nigeria wanda Sheikh Zakzaki ke jagoranta dan zama a tattauna a gane ina Matsala tare da magance ta ya zama daga karshe an samu fahimtar juna a tsakani.
~ Kuma Alhmdlh hukuma ta karbi wannan kira da yayi Wanda ta fara shiri dan samun tattaunawa tsakanin ta da Harkar tare da fahimtar juna a tsakani.
~ Shugaban Jumhuriya yayi kokari wajen ganin an samu tattaunawa tsakanin Harka da Hukuma.
~ Fatan mu Allah ka kare shi, tare da bashi karfin gwiwa cikin abubuwan da yake gabatarwa, ya kuma sakawa mataimakan shi Sheikh Saleh da Sheikh Bashir wadanda duk wani ci gaba dasu ake Samar dashi, Allah ka kare su.
✍🏿 Wannan fassarar rubutun Sheikh Balarabe yakasai ne, wanda ya rubuta da harshen larabci, ni Imran Darussalam na fassara tare da qarin wasu nuqdudi kan rubutun shi.
imrandarussalam99@gmail
24 October 2019
Post a Comment