*JAWABIN BAYAN TARON MAULUDIN KHATMA TA MU'SSASAR RASULUL A'AZAM (RAAF) ASABAR 4/12/2021*

 *JAWABIN BAYAN TARON MAULUDIN KHATMA TA MU'SSASAR RASULUL A'AZAM (RAAF) ASABAR 4/12/2021*




JAWABIN BAYAN TARO


Da Sunan Allah Mai Rahma Mai Jinkai


A daidai wannan rana, wannan kungiya mai albarka tana godiya ga Allah Ta'ala da Ya kawo ta gama babban taron Mauldinta na shekara ta 2021 a garin Dawąnau ta Jihar Kano cikin nasara. Allah Ya maimaita mana, Ya Karawa Annanbi (SAWA) daraja da daukaka. 


Kamar yadda ta saba a kowace shekara, kungiyar tana *gabatar da kiraye-kiraye ga mambobinta, da al'ummar Musulmi, da gwamnatoci, da 'yan Nijeriya gaba daya* kamar haka:


1. Kira ga al 'ummar Nijeriya gaba daya da su ci-gaba da *daukan matakan kariyar kai daga cutar Corona*, bisa bin hanyoyin kare-kai da kwararru suka tabbatar, don tabbatar da kariya ga kawukansu da iyalansu da gina kasa mai lafiya. An dade ana cewa Rigakalī ya fi Magani.


2. A daidai lokacin da muke fahimtar irin wahalhalun da gwamnatin tarayya take fuskanta na matsalar tattalin arzikin da ya shafi duniya a sakamakon cutar Corona, muna kuma kira gare ta da ta yi nazari mai zurfi a kan *batun janye tallafin man fetur,* da irin halin kunci da matsi da haka zai iya jefa talaka a ciki, wanda ke fuskantar halin fatara da hauhawar farashin kayan masarufi. 

Hakazalika muna jaddada goyon baya a kan daukar matakan bunkasa tattalin arzikin Kasa da saukaka gudanarwa.


3. Muna isar da ta'aziyya da jaje ga iyalai da mutanen da sababin *matsalolin tsaro na yin garkuwa da mutane da hare hare kan-mai-uwa-da-wabi* ya rutsa da su a wasu sassan Kasar nan, masamman a jahohin Zamfara, Katsina,

Naija da Kaduna; tare da rokon Allah Ya jikan wadanda suka mutu a sakamakon haka, Ya kuma musanya wa wadanda suka yi hasarar dukiyoyi da kadarorinsu, Ya gaggauta ceton wadanda suke hannun masu garkuwa da

mutane a halin yanzu, kuma Ya kawo mana karshen wannan matsala cikin gaggawa.


4. A kan haka, muke kira ga gwamnatoci da jami'an tsaro wadanda alhakin kare rayuka da dukiyoyin 'yan Nijeriya ya hau kansu, da su *kara kaimi wajen fuskantar lamarin tsaro* da ya addabi wadannan sassa da Kasa gaba daya. Muna yabawa kokarin da suke yi, sai dai muna kira ne da karin kaimi saboda talakawan wadannan yankuna da kasa gaba daya suna cikin tashin hankali matuka.


5. Muna kira zuwa ga jama'a da su *taimaka wa jami'an tsaro da masu kokarin shawo kan matsalar tsaro* da dukkan taimakon da suke bukata don saukaka ayyukansu da kawo Karshen matsalar tsaro a kasar nan.


6. Muna jaddada kira zuwa ga al'ummar Musulmi da su rungumi *karantarwar Musulunci na hadin-kai da fahimtar juna.*


7- Hakazalika muna kira ga Musulmi da su zama cikin masu *ciyar da kasa gaba da ci-gaba da zaman lafiya* da sauran al ummar kasa, don gina nagartacciyar Nijeriya mai zaman lafiya da lumana.


8. Kira ga jama'a da su guji *siyasantar da harkokin tsaro,* saboda wata barna ce ga dukkan mutane, ba tare da la'akari da bambance-bambancen su na siyasa ko addini da kabila ba.


9. Kira ga mambobin wannan kungiya da su ci-gaba da zama *masu bin doka da oda a duk inda suke*; su himmatu da *ilimantar da kansu da iyalansu* ta fuskokin ilimin addini da na boko, su riki hanyoyin *bunkasa tattalin arzikinsu,* su *shiga cikin ayyukan gina kasa da kawo zaman lafiya* ta dukkan fuskoki.


10- Allah ya bunkasa arziki a wannan gari na Dawanau da jihar Kano da Nigeria gaba daya.


Allah Ya kare mu da kasar mu baki daya.


Bisslam.


*Muh'd. Sani Zariya*


*Babban Sakatare*


04/12/2021

Post a Comment

Previous Post Next Post